Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahlulbayt (As) - ABNA - ya habarta cewa: An ji karar fashewar wasu abubuwa a larduna da dama
Gidan rediyon sojojin Isra'ila ya nakalto majiyar soji cewa Isra'ila ta kai wani samame a wata unguwa a Tehran babban birnin kasar Iran, inda manyan kwamandojin dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) suke.
Bayan tashin bama-bamai a wasu yankuna na Tehran, rahotanni sun nuna cewa an ji karar fashewar wasu abubuwa a wasu larduna da dama da suka hada da Kermanshah da Lorestan.
sannan an tabbatar da kai hari kan hedkwatar IRGC da ke Tehran Inda aka sanar da yiwuwar shahadantar da Janar Salami, Janar Gholamali Rashid, Dr. Tehranchi, Fereydoun Abbasi, da...
A gefe guda kuma Tashar talabijin ta Channel 14 ta Isra'ila: Jiragen saman sojojin tsaron Isra'ila sun kaddamar da wani sabon salon kai hare-hare kan Iran.
Your Comment